Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin ba ta taba yin shisshigi a harkokin cikin gidan Amurka ba
2020-09-12 16:59:16        cri
Kasar Sin bata taba yin katsalandan a harkokin cikin gidan Amurka ba, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, shine ya bayyana hakan a taron manema labarai bayan kammala tattaunawa da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov.

Wang yace, kasar Sin ba ta taba tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen duniya ba, kuma, haka kuma ba ta taba yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar Amurka ba, ya kara da cewa, wannan shine al'adar yadda take tafiyar da mu'amalarta da kasashen duniya, wanda kuma shine hakikanin tsarin tafiyar da huldar kasa da kasa mafi dacewa.

Ya ce, yanzu lokaci yayi da kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina yin shisshigi a harkokin cikin gidanta.

Majalisar wakilan jama'ar kasar ba ta taba tattaunawa ko kuma bijiro da wani batu dake shafar al'amurran cikin gidan Amurka ba, amma a taron majalisar wakilan Amurka sun sha zartar da kudirorin doka game da al'amurran cikin gidan kasar Sin.

Wang Yi yace, Amurka tana neman wuce iyaka, ya kara da cewa, ya kamata wasu mutanen Amurka su mayar da hankali kan al'amurran dake shafar kasarsu a matakin farko, su yi kokarin mutunta dokokin dake shafar huldar kasa da kasa, kuma su guji yin shisshigi a harkokin cikin gidan sauran kasashen duniya.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China