2020-08-31 11:05:20 cri |
A cikin jawabinsa, Wang ya jadadda cewa, Sin tana tsayawa tsayin daka kan matsayi mai shimfida zaman lafiya a duniya, kuma tana kokarin ba da nagartacciyar gudunmawa kan sauyawar halin da ake ciki a duniya. Ya ce Sin tana iyakacin kokarin kiyaye zaman oda da dokar kasa da kasa da ba da tabbaci ga tsarin daidaita harkokin duniya. Ban da wannan kuma, Sin na ingiza tsarin dunkulewar duniya da goyon bayan bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya.
Wang Yi ya yi nuni da cewa, hanyar da kasar Sin take bi na biyan bukatun jama'arta biliyan 1.4, ta dace da manufar samun bunkasuwa cikin lumana, kuma ba kasar Sin kadai ba, duniya baki daya na cin gajiyarta. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China