Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi zai ziyarci kasashen Turai biyar
2020-08-24 20:55:26        cri

Dan majalissar gudanarwar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai gudanar da ziyarar aiki a kasashen Turai biyar, tsakanin ranekun Talata 25 ga watan Agustar nan, zuwa 1 ga watan Satumba dake tafe.

Da yake tabbatar da hakan ga taron manema labarai na rana rana da ake gudanarwa, kakakin ma'aikatar wajen Sin Zhao Lijian, ya ce kasashen da Mr. Wang zai ziyarta sun hada da Italiya, da Netherlands, da Norway, da Faransa da Jamus, bisa gayyatar gwamnatocin su.

Ziyarar da Wang Yi zai gudanar ta wannan karo, za ta kasance ta farko da zai aiwatar, tun bayan sauki da aka samu game da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, matakin da kuma ya samu karbuwa matuka daga kasashen, tare da kara haskaka muhimmancin da sassan ke dorawa kan dangantakar Sin da kasashen kungiyar tarayyar Turai ta EU.

Zhao Lijian ya kara da cewa, Sin na fatan karkashin wannan ziyara, za ta cimma nasarar kudurori 3, wato da farko, yin hadin gwiwar aiwatar da manufofin da shugabannin Sin da na EU suka amincewa, da aiwatar da ajandojin siyasa da na tattalin arziki da cinikayyar sassan biyu. Sai kuma batun zurfafa hadin gwiwar Sin da Turai wajen kyautata yanayin da ake ciki, game da yaki da cutar COVID-19, da saisaita tsarin ayyukan masana'antu. Da kuma magana da murya guda, wajen kare tsarin cudanyar sassa daban daban, da inganta tsarin jagoranci na duniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China