Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bunkasar GDPn kasar Gambia zai ragu daga kaso 6 zuwa 2 bisa dari sakamakon bullar COVID-19
2020-09-18 09:52:07        cri
Shugaban kasar Gambia Adama Barrow, ya ce bunkasar GDPn kasarsa zai ragu daga kaso 6 zuwa 2 bisa dari, sakamakon bullar COVID-19 wadda ta yi mummanar barna ga tattalin arzikin kasar na bana.

Shugaba Barrow ya bayyana hakan ne ga 'yan majalissar dokokin kasar a jiya Alhamis, cikin jawabinsa na shekara a birnin Banjul, inda ya ce annobar COVID-19 ta yi tarnaki ga aiwatar da tsare-tsaren samar da ci gaba da gwamnatinsa ta shirya aiwatarwa a shekarar nan ta 2020.

Mr. Barrow ya kara da cewa, Gambia ta fuskanci tafiyar wahainiya a fannin ci gabanta, sakamakon raguwar harkokin tattalin arziki, mai nasaba da bullar annobar COVID-19. Ya ce bisa hasashen farko-farko, akwai yiwuwar ci gaban GDPn Gambia ya ragu daga kaso 6 zuwa kaso 2 bisa dari.

Kaza lika a cewar shugaban, raguwar hajojin da ake shigowa da su kasar daga ketare, zai haifar da gibi ga harajin kwastam, da sauran harajin da kasar ke samu daga shigo da kaya. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China