Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta ba da gudunmawar motoci biyu da kayayyakin kiwon lafiya ga kasar Gambia
2020-03-11 11:08:32        cri
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Banjul a ranar Talata ya bayar da gudunmawar motoci biyu, da na'urori da kuma kayayyakin kiwon lafiya ga ma'aikatar lafiyar kasar Gambiya, wadanda za su tallafawa kasar don inganta ayyukan kiwon lafiya.

Modou Njie, daraktan sashen bunkasa kiwon lafiya da ilmantar da alluma na ma'aikatar lafiyar kasar, ya ce gudunmawar za ta taimakawa kasar wajen cike gibin da ake da shi wajen isar da muhimman kayayyakin kiwon lafiya zuwa yankunan karkara.

Modou ya ce suna da likitoci, da nas-nas, kuma suna da kwararrun masana kiwon lafiya a asibitoci, a dukkan bangarorin asibitin koyarwa na Edward Francis (EFSTH) dake Banjul da babban asibitin Serekunda dake Kanifing. Amma hanyoyin da za'a isa zuwa asibitocin shi ne babban kalubale, don haka wadannan motoci za su taimaka wajen magance matsalolin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China