Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar zaben Gambia ta sanar da ranar zaben shugaban kasar na 2021
2020-07-16 14:00:03        cri
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Gambiya IEC, ta fitar da jadawalin babban zaben kasar na shekarar 2021 inda ta tsaida kuririn gudanar da zaben shugaban kasar a ranar 4 ga watan Disambar shekarar 2021.

A sanarwar da hukumar IEC ta fitar, za'a gudanar da zaben fidda sunayen 'yan takarar shugabancin kasa daga ranar 30 ga watan Oktoba zuwa 5 ga watan Nuwambar 2021, yayin da za'a gudanar da gangamin yakin neman zaben shugaban kasar tsakanin 9 ga watan Nuwamba zuwa 2 ga watan Disamban shekarar 2021, yayin da 4 ga watan Disambar 2021 ta kasance a matsayin ranar zabe.

Hukumar zaben tace, za'a fara rijistar mazu zabe daga ranar 14 ga watan Janairu inda za'a kammala a ranar 26 ga watan Fabrairun badi, yayin da za'a gudanar da zaben raba gardamar kan sabon kundin tsarin mulkin kasar a ranar 5 ga watan Yunin shekara mai zuwa.

An gudanar da zabe na karshe a kasar a ranar 1 ga watan Disambar shekarar 2016, inda tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya haifar da cece kuce, zaben da ya kawo karshen mulkinsa na tsawon shekaru 22. Lamarin ya jefa kasar cikin halin rashin tabbas yayin da dubban 'yan kasar suka kauracewa muhallansu kafin daga bisani tsohon shugaban ya nemi mafaka a kasar Equatorial Guinea.

Shugaban kasar Adama Barrow wanda ya gaji Jammeh, ya samu goyon bayan gamayyar jam'iyyun siyasar kasar 7. Yayi alkawarin shugabantar kasar na tsawon shekaru uku kana daga bisani yayi murabus, sai dai ya sauya alkawarin da ya dauka tun da farko, lamarin da ya haifar da zanga zanga da tashin hankali a kasar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China