Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gambia ta nuna rashin jin dadi kan takunkumin da Amurka ta sanyawa jami'an ICC
2020-09-06 17:00:06        cri
Gwamnatin kasar Gambia ta bayyana rashin jin dadinta bisa matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na kakabawa wasu manyan jami'an kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC biyu.

Amurka ta sanya takunkumi kan babban mai gabatar da kara na kotun ICC Fatou Bensouda, wanda dan asalin kasar Gambia ne, da kuma wani babban jami'in kotun, a matsayin mayar da martani game da tuhumar da jami'an suka gudanar kan zargin wasu sojojin Amurka da aikata laifukan yaki a Afghanistan.

Takunkumin ya hada da rike duk wasu kadarori da dake Amurka ko kuma suke karkashin ikon Amurka, mallakar Bensouda, da shugaban gudanarwar sashen hadin gwiwa na kotun ta ICC, Phakiso Mochochoko. Sannan duk wasu mutane ko hukumomin da suka cigaba da yin wata huldar kudi tare da Bensouda da Mochochoko, su ma zasu iya fuskanatar barazanar takunkumin, kamar yadda gwamnatin Amurka ta sanar.

A cewar gwamnatin Gambiya, wannan mataki na Amurka mummunan saba doka ne, kuma yunkuri ne na kawo cikas da neman taka birki game da muhimman ayyukan kotun ICC a yakin da take yi wa masu aikata manyan laifuka a kasa da kasa.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China