Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An killace ministan lafiyar kasar Gambia
2020-08-05 10:31:20        cri
Rahotanni daga kasar Gambia na cewa, an killace ministan ma'aikatar lafiyar kasar Amadou Samateh, kana an tabbatar da harbuwar magajin garin Kanifing Talib Ahmed Bensouda da cutar numfashi ta COVID-19.

Mr. Samateh ya shiga cibiyar da aka tanada domin killace wadanda ake zaton sun harbu da cutar ne a jiya Talata, bayan wasu ministocin kasar su uku sun harbu da cutar a baya, ministocin dai sun hada da na kudi Mambury Njie, da na makamashi Fafa Sanyang, da na ma'aikatar noma Amie Fabureh.

To sai dai kuma, wata sanarwa da ma'aikatar lafiyar kasar ta fitar, ta ce minista Samateh na cikin kyakkyawan yanayin lafiya, kuma ba a kai ga samun cikakken sakamako na gwajin da aka yi masa ba tukuna. Sanarwar ta ce yayin da yake jiran sakamakon, Samateh zai ci gaba da aiki daga inda aka killace shi.

A daya bangaren kuma, wata sanarwa da ofishin shugaban kasar ta Gambia Adama Barrow ya fitar, ta tabbatar da killace magajin garin Kanifing Talib Ahmed Bensouda, bayan an tabbatar da harbuwar sa da cutar. Tun a makon jiya ne dai magajin garin ya killace kan sa, bayan da aka samu labarin harbuwar mataimakin shugaban kasar da cutar.

Alkaluman hukumar lafiyar kasar sun nuna cewa, Gambia na da mutane 671 da aka tabbar suna dauke da COVID-19, ciki hadda mutane 14 da cutar ta hallaka, da kuma wasu 79 da suka warke. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China