Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta bayar da tallafin kayayyakin kiwon lafiya don yaki da COVID-19 a Sudan ta kudu
2020-09-05 16:12:01        cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO a ranar Juma'a ta aike da tallafin kayayyakin kiwon lafiya na sama da fam miliyan 85 na kudin kasar Sudan ta kudu, wato kwatankwacin dala miliyan 5.2, domin taimakawa kasar ta gabashin Afrika a yakin da take yi da annobar COVID-19.

Alain Noudehou, jami'in shirin bayar da jin kai a kasar Sudan ta kudu, ya ce, hukumar WHO ta samar da kayayyakin kiwon lafiya ton 70 wanda ta yi amfani da kudaden asasun ayyukan jin kai na kasar wato SSHF da kuma na bankin raya ci gaban Afrika AfDB, wajen sayen kayayyakin.

Noudehou ya fada cikin wata sanarwa da aka fitar a Juba cewa, tallafin sun hada da kayayyakin bayar da kariya, da takunkumin rufe fuska, da gilashin kare fuska, da na'urar taimakawa numfashi, da rigunan da jami'an lafiya ke amfani da su da gilashin da suke kare fuskarsu.

Ya ce, tallafin kayayyakin lafiyar za su taimakawa ma'aikatan lafiya kasar wajen ba su kariya daga kamuwa da cutar a lokacin da suke kula da lafiyar majinyatan da suka kamu da annobar ta COVID-19.

Noudehou ya kara da cewa, akwai bukatar tabbatar da bayar da kariya ga ma'aikatan lafiyar dake bakin aikinsu na tallafawa lafiyar mutanen Sudan ta kudu. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China