Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rikicin da ya barke tsakanin 'yan gudun hijirar Sudan ta kudu a Uganda yayi sanadin hasarar rayuka
2020-07-20 11:48:41        cri
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta sanar cewa, 'yan gudun hijirar Sudan ta kudu uku sun rasa rayukansu a kasar Uganda, sannan an raunata wasu mutanen 6, kana daruruwan mutane sun kauracewa muhallansu sakamakon rikicin kabilanci da ya barke a sansanin 'yan gudun hijira dake Palorinya, a arewa maso yammacin gundumar Obongi.

Ofishin babban jami'in hukumar kula 'yan gudun hijirar MDD, UNHCR ya sanar da cewa, tashin hankalin da ya barke tsakanin kabilun Sudan ta kudu ya faru ne a ranar 13 ga watan Yuli sakamakon satar amfanin gona a kauyen Dama.

UNHCR ya ce, sama da tantuna 280 aka cinnawa wuta, lamarin da ya tilastawa wasu iyalai tserewa zuwa wasu makarantun firamare dake makwabtaka da sansanin, da wasu ofisoshin gwamnati, da na 'yan sanda domin neman tsira.

Hukumar kula da 'yan gudun hijirar tace, koda yake rikicin ya lafa tun a ranar Laraba, amma har yanzu akwai zaman dar dar. Kimanin mutane 30 aka kama kuma ana tsare da su a halin yanzu a ofishin 'yan sanda dake gundumar Obongi.

Joel Boutroue, wakilin hukumar UNHCR dake Uganda, yace sun yi matukar bakin ciki da faruwar tashin hankalin wanda yayi sanadiyyar hasarar rayuka, ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan mutanen da aka kashe a rikicin.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China