Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta kudu ta zargi kungiyar 'yan adawa da sace fararen hula sama da 100
2020-04-07 11:16:40        cri
Rundunar sojan kasar Sudan ta kudu, ta tabbatar cewa, kungiyar 'yan adawa ta NAS karkashin jagorancin janar Thomas Cirilo da ya yi ridda dake jihar Yei-River mai makwbtaka da kasar Uganda, ta yi awon gaba da fararen hula sama da 100.

Mai Magana da yawun rundunar sojan Sudan ta kudu(SSPDF) Lul Ruai Koang wanda ya sanar da haka, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Juba cewa, bayanan da suka samu kimanin makon da ya gabata, sun nuna cewa, dakarun NAS sun tarwatsa sansanoninsu da nufin daukar matasa aiki a wadannan yankuna, kuma da alamu wadannan matasa da NAS ta sace tana son su zama mata mayaka ne.

A cewar gidan rediyon Tamazuj na kasar Sudan ta kudu, rundunar NAS ta karyata hannu wajen sace mutanen. Maimakon haka ma, kungiyar ta zargi dakarun gwamnati da sace fararen hula.

A lokuta da dama a baya, SSPDF ta sha zargin dakarun NAS da keta yarjejeniyar zaman lafiya ta hanyar yiwa fararen hula kwanton bauna a kan manyan hanyoyin jihar YEI River, dake kudu maso yammacin Juba, babban birnin kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China