Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Sama da fararen hula 800 aka kashe a Sudan ta kudu a rubu'i na biyu na bana
2020-08-28 11:15:54        cri
Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Sudan ta kudu UNMISS, ya sanar cewa, a kalla fararen hula 887 aka hallaka a Sudan ta kudu tsakanin watan Afrilu zuwa Yunin wannan shekara.

Sashen kare hakkin dan adam na UNMISS, ya tattara alkaluma sama da 417, wanda ya kunshi fararen hula kimanin 1,620 a rubu'i na biyu na wannan shekara, kamar yadda rahoton da hukumar ta fitar a Juba ya nuna.

Hukumar wanzar da zaman lafiyar ta MDD tace, an kashe fararen hula a kalla 887, an jikkata wasu 531, an yi garkuwa da 176, kana an ci zarafin wasu 26 ta hanyar lalata a fadin kasar a rubu'i na biyu na bana. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China