Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sudan ta kudu ta damu da yadda Ebola ke yaduwa a lokacin COVID-19
2020-08-24 10:29:00        cri
Kasar Sudan ta kudu ta sanar a jiya Lahadi cewa, tana sanya ido kan yadda jama'a ke kai koma a kan iyakar kasar da Jamhuriyar demokiradiyar Congo (DR Congo), domin dakile yaduwar Ebola, a wannan lokaci da duniya ke fama da annobar COVID-19.

Mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar kasar Thuou Loi, ya bayyana cewa, Sudan ta kudu ta tsaurara matakan hana yaduwar cutar Ebola a kasar, da yanzu haka take fama da wadanda ke kamuwa da COVID-19.

Loi ya ce, Ebola abin damuwa ne, wannan ne ma ya sa wata tawagar lafiya, take kokarin tabbatar da cewa, an tsaurara matakan kandagarki, domin ganin an magance duk wasu batutuwan kiwon lafiyar jama'a da suka damu duniya, kamar cutar Ebola, Covid-19 da sauran cututtuka masu yaduwa.

Shi ma wakilin WHO a Sudan ta kudu, kana jami'in tsare-tsaren kiwon lafiya na kasa da kasa, Joseph Francis Wamala ya bayyana cewa, an sanya kasar Sudan ta kudu cikin mataki na biyu na kasashen da za su shiryawa cutar Ebola, saboda nisanta daga yadda cutar ta bulla a halin yanzu kilomita 4,000 ne kawai. Ya zuwa yanzu dai, cutar ta yadu zuwa larduna 11 cikin 17 dake shiyyar. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China