Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta kudu ta ce ana shirin kafa majalisar zartaswar gwamnatin hadin kan kasar
2020-03-12 13:11:36        cri

Sudan ta kudu ta sanar a ranar Laraba cewa ana shirye-shiryen kafa majalisar zartaswa karkashin gwamnatin hadin kan kasar.

Abdon Agaw Jok, babban sakataren gwamnatin kasar Sudan ta kudu, ya ce bangarorin dake aikin kafa gwamnatin hadin kan kasar sun kammala zaben mutanen da za'a nada a mukamai na majalisar zartaswar kasar.

Jok ya ce, shugabannin sun amince za'a rarraba mukaman ministoci ga bangarorin kasar kuma kawo yanzu an kammala zabar wasu daga cikin sunayen mutanen da za'a nada a mukaman ministocin wanda ake sa ran bayyana sunayen ministocin da za su jagoranci majalisar zartaswar gwamnatin hadin kan kasar nan da wasu kwanaki masu zuwa a Juba.

Ya ce abin da ya kawo jinkiri shi ne, wasu daga cikin bangarorin dake shafar yarjejeniyar zaman lafiyar kasar ta watan Satumbar 2018 ba su kammala amincewa da sunayen ministocin da 'yan majalisun da ake son nadawa don su jagoranci gwamnatin hadin kan kasar ba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China