Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mike Pompeo da mabiyansa suna kan hanyar zama 'yan iska a fannin siyasa
2020-07-29 21:52:34        cri

 

Kwana nan, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo, da shugaban hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayyar kasar Amurka wato FBI Christopher Wray, da mashawarcin shugaban kasar a fannin tsaron kasa Robert O'Brien, sun ba da jawabi daya bayan daya, don nuna adawa da kasar Sin, inda dukkansu suka bata sunan kasar Sin da cewa, wai ta "sace" ikon mallakar fasaha ta kasar Amurka, sun kuma yi zargi kan daliban kasar Sin, da ma'aikatan kasar, bisa mummunan buri na musamman a kasar. Har ma a 'yan kwanakin da suka wuce, kasar Amurka ta rufe karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake Houston bisa wannan dalili, wanda hakan ya illata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Ana iya gano cewa, bisa yanayi mai tsanani da dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka take ciki, tun bayan kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu, masu mulkin Washington suna ta yayata rade-radi kamar wai "Masu leken asari na Sin", sun yi haka ne da nufin mayar da sabani a cikin kasar da la'akari da siyasar zabe. Ban da wannan kuma, suna da burin tsoratar da al'ummar kasar don cimma burinsu na musamman na nan gaba.

 

Yanzu dai, bisa karuwar karfin kasar Sin a fannin kimiyya da fasaha, 'yan siyasan kasar Amurka dake bin ra'ayin samun riba kan asarar wani bangare suna ta damuwa kan wannan, don haka, a yayin da suke yayata rade-radi na wai "Kasar Sin ta sace fasahohin kasar Amurka", a sa'i daya kuma suna amfani da dalilinsu na wai "kiyaye tsaron kasa" don saka takunkumi kan kamfanonin kasar Sin ba bisa tushe ba, ta yadda za su iya kiyaye matsayin mallaka da kasar Amurka ke dauka a fannin kimiyya da fasaha. Matakin da suka yi, ya cire marufin fuskarsu na "yin takara cikin 'yanci". (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China