Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin Ta Tsai Da Kudurin Rufe Karamin ofishin Jakadancin Amurka A Chengdu Domin Mayar Da Martani Kan 'Yan Siyasan Amurka
2020-07-24 19:44:28        cri

Yau Jumma'a ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da ofishin jakadancin kasar Amurka da ke kasar Sin cewa, Sin ta tsai da kudurin rufe karamin ofishin jakadancin Amurka dake birnin Chengdu, tare da dakatar da dukkan ayyukansa da harkokinsa. Kasar Sin ta dauki wannan mataki ne, biyo bayan kudurin Amurka na rufe karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake Houston. Kasar Sin dai ta nuna adawa da matakin na Amurka, abin da ya sa ita ma ta dauki irin wannan mataki bisa doka. Kasar Sin ta dauki wannan mataki ne ba domin jama'ar Amurka ba, a'a, ta mayar da martani ga wasu Amurkawa masu son kai wadanda suke adawa da kasar Sin. Kasar Sin tana kiyaye mutuncinta da hakkinta, matakin da ta dauka ya dace da ka'idojin diflomasiyya, ya zama dole kuma ya yi daidai.

Kasar Sin na tsayawa kan samun ci gaba cikin lumana, amma ba za ta ja da baya wajen kiyaye 'yanci, da tsaro da muradun raya kasarta ba. Matakin da ta dauka a wannan karo ya alamta cewa, jama'ar Sin ba su son ta da fitina, amma ba sa jin tsoron mayar da martani, idan aka nemi tayar mata da fitina. Kasar Sin ba za ta sauya aniyarta ta kiyaye halaltattun hakkokinta ba.

Yanzu haka sakamakon abubuwa na rashin kunya da 'yan siyasan Amurka suka yi, ya sa Sin da Amurka suke fuskantar kalubale mafi hadari wajen raya huldarsu tun bayan kulla huldar jakadanci a tsakanin kasashen 2. Yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 yana kawo musu alheri duka, a hannun guda kuma nuna adawa da juna, shi ma zai kawo musu illa. Hadin kan kasashen 2, ita ce hanya daya kacal da za su iya bi. Wannan shi ne abubuwan da aka koya daga tarihi, kuma manufa ce da za a iya bi a nan gaba. A don haka, ya kamata wasu daga 'yan siyasan Amurka da suke yunkurin mayar da tarihi koma baya su dakatar da abubuwan da suke yi. In ba haka ba, kasar Sin za ta mayar da martani, kuma hakan na iya zubar musu da kima a idon duniya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China