Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yaushe Ne 'Yan Siyasar Amurka Da Ke Yunkurin Dorawa Wasu Laifi Za Su Fara Yaki Da Annobar COVID-19 Ta Hanyar Kimiyya?
2020-07-25 17:16:35        cri
Ko da yake shugaban kasar Amurka bai gaji da bata sunan kasar Sin dangane da salin annobar cutar numfashi ta COVID-19 ba, amma mutane sun gaji da yadda yake kiran annobar da sunan "Chinese virus" da "Kung Fu Flu" a wurare da dama, a yunkurin rura wutar nuna bambanci a tsakanin al'umma. Abin da ya yi ya sa jama'ar Amurka da na kasashen duniya yin tir da shi. An yi nuni da cewa, karuwar masu kamuwa da annobar ta COVID-19 a Amurka da kuma barkewar rikici sakamakon nuna bambanci tsakanin al'umma sun haddasa matukar damuwa a tsakanin 'yan siyasan Amurka. Ba yadda za su yi, sai sun maimaita abubuwan da suka yi a baya, sun dorawa wasu laifi, a yunkurin karkatar da hankalin jama'arsu kan sauran batutuwa, da kuma biyan bukatun yakin zabe.

Sanya siyasa a gaban kimiyya kan sadaukar da rayukan mutane. Amma abin bakin ciki shi ne, yayin da yawan masu kamuwa da annobar ya wuce miliyan 4 a Amurka tare da yin asarar rayukan mutane fiye da dubu 140, 'yan siyasar kasar masu son kai sun mayar da hankali kan harkokin siyasa kadai, ba su sauke nauyin dake bisa wuyansu ba, amma sun yi dabara sun dora wa kasar Sin laifi maimakon fara yaki da annobar ta hanyar kimiyya. Wannan abun bakin ciki ne, kuma abin tausayi ga jama'ar Amurka. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China