Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jawabin Mike Pompeo ya gamu da suka daga sassan duniya
2020-07-28 14:49:12        cri
A makon jiya ne Mike Pompeo, sakataren harkokin wajen kasar Amurka ya yi jawabin nuna adawa da kasar Sin a bainar jama'a, inda ya yi shelar cewa, manufar Amurka ta yin mu'amala da kasar Sin ba ta yi nasara ba, a yunkurin bata huldar da ke tsakanin Sin da Amurka bisa tunanin yakin cacar baki. Kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya da kwararru sun yi tir da Mike Pompeo da wasu 'yan siyasa irinsa. Kana akasarin ra'ayoyin jama'a na kasa da kasa sun yi adawa da sabon tunanin yakin cacar baki.

A ranar 26 ga wata, kafar watsa labarun masu sayayya da kasuwanci na Amurka wato CNBC ya ruwaito cewa, a kwanan baya Mike Pompeo ya gabatar da jawabi, inda ya nuna adawa da kasar Sin, yayin da gwamnatin Trump ta kara daukar matakan nuna tsattsauran ra'ayi, lamarin da ya bayyana halin da ake ciki yanzu a matsayin sabon yakin cacar baki. Sakamakon tsokanar da Amurka ta tayar, ya sa kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya suka rika yin fito-na-fito mai hadari a tsakaninsu. Matakin nuna cin gashin kai da Amurka ta dauka ya jefa duniya cikin wani hali na rashin tabbas

A ranar 26 ga wata, jaridar Los Angeles Times ta ce, jawabin Pompeo ya sauya huldar dake tsakanin Amurka da Sin sosai. A goman shekaru da suka wuce, Sin da Amurka sun kau da sabani a tsakaninsu, sun yi kokarin cimma ra'ayi daya yayin da suka jingine sabaninsu a gefe guda. Suna hada kansu a fannonin tabbatar da kwanciyar hankali a tattalin arzikin duniya, daidaita sauyin yanayi da yin rigakafin cututtuka masu yaduwa da dai sauransu. Amma yanzu ga alama, zamani ya sauya. Kwararru da masu tsara manufofi wadanda suka dade suna nazarin huldar da ke tsakanin Sin da Amukar, suna kuma himmantuwa wajen kokarin kafa dankon zumunci a tsakanin kasashen 2 suna ganin cewa, gwamnatin Trump tana kokarin ta da wani sabon salon yakin cacar baki, ba su so yin tattaunawa, abubuwan da suke yi suna da hadari sosai, wadanda kila za su haddasa rikici baki daya. Sa'an nan kuma an fahimci rashin gaskiyarsu matuka, wadanda suka yi shelar cewa, suna kula da jama'ar kasar Sin.

A ranar 25 ga wata, jaridar The New York Times ta wallafa wani sharhi dake cewa, gwamnatin Trump tana haddasa rudani. Jami'an gwamnatin sun shirya daukar tsattsauran matakai wajen haifar da wani yanayi, inda za a dade ana yin fito-na-fito da kuma takara da kasar Sin. Saboda suna ganin ba za su yi nasara a babban zaben da za a yi ba, shi ya sa suke yunkurin bata huldar da ke tsakanin Amurka da Sin, lamarin da zai addabi wadanda za su ci babban zaben. Sharhin ya nuna cewa, Pompeo ya bata sunan Amurka, wanda Amurka ta dauki shekaru fiye da 200 tana ginawa.

Jaridar Financial Times ta kasar Burtaniya ta bayyana jawabin Pompeo a tamkar wani jawabin yakin babban zabe. Basirar wannan dan siyasa mai hadama tana raguwa.

Kamfanin dillancin labaru na Bloomberg ya ruwaito a ranar 27 ga wata cewa, Ray Dalio, wanda ya kafa kamfanin zuba jari na Bridgewater ya yi kashedi da cewa, yadda Amurka take ta da yakin ciniki, yakin fasaha, yakin siyasa, da nuna bambancin tunani a gida, yana haddasa mata koma-bayanta.

Michael Swaine, babban manazarci a kwalejin nazarin zaman lafiya na duniya na Carnegie ya bayyana ra'ayinsa kan shafin sada zumunta cewa, gwamnatin Amurka maras jin kunya ita ce ta haddasa hadarin da muke gani yanzu. Yadda ta rufe karamin jakadancin kasar Sin a Houston, wani irin yunkuri ne da 'yan siyasar kasar suka yi don ceton Trump a harkokin siyasa. Amurka ce a kullum take haddasa duk wata matsala. Ana fatan ba za ta cuci kasar Sin ba. Amurka ta yi shelar ta da sabon yakin cacar baki, amma ba ta tsara manufofi ba. Mafarki ne kawai take yi.

Stephen John Hadley, tsohon mashawarcin Amurka kan tsaron kasa yana ganin cewa, gwamnatin Amurka tana bukatar tsara manyan tsare-tsare masu dorewa dangane da yin mu'amala da kasar Sin, a kokarin kafa wani tsarin yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2, tare da wani sharadi na farko, wato ba za a kawo rarrabuwa a duniya ba, kuma ba za a ta da yaki ba.

A ranar 25 ga wata, kwararru daga kasashen Amurka, da Sin, da Burtaniya da sauran kasashe 45 sun halarci taron duniya ta kafar bidiyo kan yin adawa da sabon yakin cacar baki. A cikin sanarwar da aka fitar bayan taro, an yi kira ga Amurka da ta yi watsi da tunanin yakin cacar baki da dakatar da dukkan matakan da suke illata zaman lafiyar duniya, kana a goyi bayan yin tattaunawa a tsakanin Sin da Amurka. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China