Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kalaman Robert Redfield Sun Karyata Zargin Da Aka Yiwa Kasar Sin
2020-07-30 15:45:31        cri
Yayin da mahukuntan kasar Amurka, da wasu daga 'yan siyasar kasar ke ci gaba da dora alhakin barkewar cutar numfashi ta COVID-19 kan kasar Sin, da ma wasu sassa na daban, a hannu guda, kwararru da masana a cikin kasar, na ci gaba da karyata irin wadannan kalamai marasa tushe ko makama.

A baya bayan nan ma, daraktan cibiyar kandagarki, da hana yaduwar cututtuka ta Amurka Robert Redfield, ya bayyana cewa, Amurka ta yi fargar-jaji, wajen tunkarar wannan annoba a lokaci mafi dacewa. Jami'in ya ce Amurka ba ta sanya lura ga yadda wannan cuta ta yadu cikin sauri a yankunan nahiyar Turai ba, lamarin da ya haifar da shigarta Amurka daga Turai, har ta kai matsayin shiga ko ina a sassan Amurka.

Wadannan kalamai dai na Mr. Redfield na zuwa ne bayan da a baya, mahukuntan Amurka suka rika dora alhakin shigar cutar, da boye bayanan ta kan kasar Sin, bayan kuwa sanin kowa ne cewa tun da fari, sai da kasar ta Sin, karkashin hukumar lafiya ta duniya WHO, ta gargadi daukacin kasashen duniya da su shiga cikin shirin ko ta kwana, don kaucewa yaduwar wannan annoba mai matukar hadari.

A kalaman Mr. Redfield, ya kuma bayyana yadda gwamnatin Trump ta yi jinkirin dakatar da tafiye-tafiye tsakanin kasashen Turai da Amurka, ta yadda hakan ya baiwa cutar cikakken lokacin shiga Amurka ba tare da wani shinge ba.

Kaza lika an takaita gwajin cutar, ta yadda masu dauke da ita da dama suka rika cudanya da sauran masu lafiya, wanda hakan ya haifar da karin masu harbuwa da ita a ko'ina cikin kasar.

Ya zuwa yau ranar Alhamis, yawan mutanen da COVID-19 ta harba a Amurka, ya kai mutane 4,568,375, kana tuni cutar ta hallaka mutane 153,845.

Abun lura a nan shi ne, kawo wannan lokaci, duk da irin wadannan dalilai, da kalaman masana ciki hadda na cikin Amurka, gwamnatin kasar da wasu 'yan siyasar ta, ba su dakatar da furta kalamai da daukar matakai na bata sunan kasar Sin ba, ko da yake dai tuni masharhanta ke alakanta matakan gwamnatin Amurkar mai ci, da wani yunkurin karkatar da tunanin Amurkawa, da nufin samun amincewarsu yayin babban zaben kasar dake tafe.

To amma dai duk da haka, tuni masu nazarin yanayin da ake ciki, suka yi amannar cewa, duk wasu kalamai, da matakai da mahukuntan Amurka ke dauka na bata sunan kasar Sin ba za su yi nasara ba. Kaza lika a hannu guda, irin wadannan bayanai da Mr. Redfield ke yi, za su ci gaba da kubutar da kasar Sin daga karairayin da gwamnatin Amurka mai ci ke yadawa, da nufin cimma bukatun kashin kai, da ribar siyasa mai karo da gaskiya, matakan da kuma ke kara gurgunta kyakkyawar alakar da aka jima da kafawa tsakanin Sin da Amurka. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China