Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya shugabanci taron ministocin harkokin wajen kasashe makwabta hudu kan tinkarar cutar COVID-19
2020-07-28 09:40:01        cri
An gudanar da taron ministocin harkokin wajen kasashe makwabta hudu wato Sin da Afghanistan da Pakistan da kuma Nepal a jiya, kan matakan tinkarar cutar COVID-19 ta kafar bidiyo, inda memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya shugabanci taron, wanda ya samu halartar mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Afghanistan Mohammed Haneef Atmar, da ministan harkokin wajen kasar Pakistan Shah Mahmood Qureshi, da ministan harkokin tattalin arzikin kasar Pakistan Khusro Bakhtyar, da kuma ministan harkokin wajen kasar Nepal Pradeep Kumar Gyawali.

Wang Yi ya bayyana cewa, a matsayinta na makwabciya kuma abokiya, kasar Sin tana son hada hannu da wadannan kasashen uku wajen tinkarar cutar COVID-19, da kiyaye lafiyar jama'a, da sa kaimi ga farfado da masana'antu, da tabbatar da zaman rayuwar jama'a har zuwa lokacin kawo karshen yaki da cutar COVID-19.

Ministocin kasashen uku sun bayyana cewa, za su yi kokari da hadin kai da kasar Sin wajen yaki da cutar COVID-19, da tabbatar da yin ciniki da jigila a tsakaninsu, da sa kaimi ga mu'amalar mutane da cinikayya da juna, da inganta shawarar "ziri daya da hanya daya" a fannin kiwon lafiya, da kuma raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China