Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin da kasashen Larabawa suna marawa juna baya
2020-07-06 21:41:51        cri
Yau Litinin, memban majalisar gudanarwa ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya halarci taron ministocin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Larabawa karo na 9, inda ya bayyana cewa, ya kamata Sin da kasashen Larabawa su tsaya ga marawa juna baya, da kiyaye adalci da gaskiya. Kasar Sin za ta kasance tare da kasashe masu tasowa, da nuna goyon-baya ga harkokin ci gaban daukacin al'umma.

Wang ya ce, kasarsa na goyon-bayan kasashen Larabawa don tabbatar da tsaron siyasa da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashensu, domin neman ci gaba da kansu. Wang Yi ya kuma godewa kasashen Larabawan saboda matsayinsu kan harkokin cikin gidan kasar Sin, inda a cewarsa, Hong Kong da Xinjiang da Taiwan, dukkansu sassa ne na kasar Sin. Kasar Sin tana adawa da duk wani yunkuri na amfani da harkokin sassan domin tsoma baki a harkokin cikin gidanta.

Wang ya kuma jaddada cewa, kasarsa ba za ta taba mantawa da babban goyon-bayan da kasashen Larabawa suka samar mata a fannin yaki da yaduwar cutar COVID-19 ba. Kana, kasar Sin tana kokarin samar da agajin kayayyaki da shirya taruka ta kafar bidiyo na kwararru da kuma tura rukunonin masana aikin jinya domin taimakawa kasashen Larabawan dakile yaduwar cutar.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China