Ministan harkokin wajen kasar Sin ya bukaci Sin da Indiya da su rika tattaunawa don wanzar da zaman lafiya a kan iyakokinsu
Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ya ba da shawarar zurfafa tattaunawa da yin mu'amala tsakanin kasarsa da Indiya, a wani mataki na magance batun kan iyaka da ma tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a kan iyakokin yankunan kasashen biyu yadda ya kamata.
Wang ya bayyana haka ne, yayin da yake zantawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Indiya S jaishankar. (Ibrahim)