Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin a Nijeriya ya gana da ministan harkokin wajen kasar
2020-04-15 10:53:20        cri

Jiya Talata, jakadan kasar Sin dake Nijeriya Zhou Pingjian ya gana da ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama, sa'an nan, sun gana da 'yan jarida cikin hadin gwiwa.

Zhou Pingjian ya ce, cikin 'yan kwanakin nan, ya ci gaba da tuntubar minista Onyeama kan matakan kandagarki da hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 da lardin Guangdong ya dauka wadanda suka shafi 'yan Nijeriya dake kasar Sin, sun kuma cimma matsayi daya kan wannan aiki. A halin yanzu, birnin Guangzhou da lardin Guangdong sun dukufa wajen yaki da cutar, ba kan 'yan kasar Nijeirya, ko 'yan kasashen Afirka ko kuma 'yan kasashen ketare ba. Ya ce kasar Sin ba ta taba nuna bambanci kan'yan kasashen ketare dake kasar ba, kuma ba ta daukar matakai masu bambanta wasu mutane na musamman. Ya kara da cewa, bisa kokarin da aka yi, an warware wasu matsalolin da 'yan Nijeriya da 'yan Afirka suka gamu da su a kasar Sin yadda ya kamata, kuma akwai wasu matsalolin da aka dukufa wajen warware su kamar yadda ake fata. A halin yanzu, kasashen duniya suna ci gaba da yaki da annobar, kuma kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwar dake tsakanita da Nijeriya domin cimma nasarar wannan yaki cikin hadin gwiwa.

A nasa bangare kuma, malam Onyeama ya ce, kwanan baya, an saurari wani sakon murya da dan kasuwar Nijeriya dake birnin Guangzhou na kasar Sin ya dauka da harshen Ibo, an kuma fassara wannan sakon murya zuwa harshen Turanci, inda aka yi cikakken bayani kan abin da ya shafa, ba kamar yadda aka bayyana cikin bidiyon da wasu kafofin watsa labarai suka bayar ba. A halin yanzu, kafofin watsa labarai na kasa da kasa suna tasiri sosai kan ra'ayoyin al'ummomin kasa da kasa, kullum akwai wasu mutane dake bayani kan wani batu bisa ra'ayoyi ko kuma moriyarsu. Ya kamata gwamnatin kasar Nijeriya da al'ummomin kasar su yi tunani kan batutuwan da abin ya shafa yadda ya kamata. Dangane da tsokacin da jami'in kasar Nijeriya ya yi cikin bidiyon cewar "An ki tsare fasfo", wannan ba daidai ba ne, mai iyuwa matsalar mu'amala ce. Gwamnatin kasar Sin tana amsa damuwa da bukatar Nijeriya yadda ya kamata, kuma ana dukufa wajen warware wannan matsala. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China