Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin StarTimes da UNESCO sun hada hannu kan gangamin yaki da labaran bogi game da COVID-19
2020-07-31 10:57:05        cri

Gidan talabijin na StarTimes na kasar Sin, ya hada hannu da hukumar bunkasa ilimi, kimiyya da raya al'adu ta MDD UNESCO, domin gudanar da gangamin yaki da yada bayanan bogi game da COVID-19.

Mataimakin shugaban kamfanin StarTimes Luis Lu, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, domin kyautata ayyukan gangamin, za a samu damar ganin hotunan bidiyo 10 da suka yi nasara a kan manhajar StarTimes ON, da mutane sama da miliyan 20 ke amfani da ita a fadin nahiyar Afrika.

Ya ce ya lura cewa, ba kalubalen lafiya kadai annobar ke tattare da shi ba, har ma da illata yanayin sadarwar yau da kullum saboda jirkita bayanai, lamarin da ka iya mummunan tasiri kan lafiyar kwakwalwa.

Ya kara da cewa, wayar da kai kan bayanai da labaran bogi game da COVID-19, zai samar da wani dandali na bayyana muhimmanci sahihan bayanai dangane da annobar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China