Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD na neman dala miliyan 61 domin tunkarar ambaliyar ruwa a Sudan ta Kudu
2019-11-09 16:20:13        cri
Ofishin dake kula da ayyukan agajin jin kai na MDD, ya ce yana bukatar a kalla dala miliyan 61 domin samar da kayayykin agaji ga dubban mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a galibin sassan Sudan ta Kudu.

Ofishin ya ce tallafin zai gaggauta samar da agaji ga mutanen da ambaliyar ta shafa a yankuna 32 dake Upper Nile da Warrap da Northern Bahr el Ghazal da Unity da Lakes da yankunan tsakiya da gabashin Equatoria, inda aka yi kiyasin ambaliyar ruwa ta rutsa da mutane 908 tun da aka shiga lokacin damina a watan Yuli.

Wata sanarwa da shugaban ofishin a Sudan ta Kudu Alaine Noudehou ya fitar a Juba, ta ce ana matukar bukatar agaji a Pibor da sauran wasu yankuna. Ya ce ruwa ya mamaye asibitoci da makarantu da mujami'u da ofisoshin 'yan sanda, kuma baki daya al'ummomin yankin sun rasa matsugunansu, kuma idan ruwan ya ci gaba da karuwa, za su kara rasa mafaka.

A kwanan nan ne Alaine Noudehou ya kammala ziyara a Pibor dake yankin Jonglei, wanda ke cikin wuraren da ambaliyar tafi muni.

A ranar 27 ga watan Oktoba ne Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kirr, ya ayyana yankunan kasar da ambiliya ta shafa a matsayin masu bukatar daukin gaggawa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China