Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
ICRC:Fadan kabilanci ya yi sanadin rayukan mutane sama da 60 a Sudan ta kudu
2019-12-06 10:19:12        cri
Kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa ta Red Cross (ICRC) ta bayyana cewa, kimanin mutane 67 ne suka gamu da ajalinsu, wasu 100 kuma suka jikkata, a wani fadan kabilanci da ya barke a jihar Western Lakes ta kasar Sudan ta kudu.

Kungiyar ta ce, ta kuma kwashe mutane 29 da suka samu raunukan harbin bindiga ta jiragen sama a fadan da ya barke tsakanin wasu kabilu biyu, kilomita 100 arewa da Rumbek.

Da yake karin haske kan lamarin, shugaban tawagar kungiyar ICRC a Sudan ta kudu James Reynolds, ya bayyana cewa, za a baiwa mutanen da aka kwashe karin kulawa a Juba.Ya kuma bayyana takaicin cewa, fadan kabilanci na ci gaba da wargaza nasarorin da aka samu a kasar.

James Reynolds, ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar a Juba, babban birnin kasar cewa, cibiyar kula da lafiya daya ce kacal, kuma babu muhimman kayayyakin kiwon lafiya da za a kula da wadanda suka ji munanan raunuka, kamar na harbin bindiga. Wannan ya sa, kungiyar ta kwashe marasa lafiyan ta jirgin sama zuwa asibitin sojoji dake Juba, don samun kulawar tawagar likitoci. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China