Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gabon, Equatorial Guinea sun mikawa AU daftarin amincewa da yarjejeniyar AfCFTA
2019-07-07 21:00:55        cri
A yau Lahadi kasashen Gabon da Equatorial Guinea suka mika daftarin bayana amincewarsu da yarjejeniyar ciniki maras shinge ta kasashen Afrika (AfCFTA) ga kungiyar tarayyar Afrika (AU).

Kasashen biyu sun mika takardun ne a lokacin bude taron kolin shugabannin kasashen mambobin AU karo na 12 wanda ke gudana a Niamey, babban birnin jamhuriyar Nijer.

Yarjejeniyar ta AfCFTA, an kaddamar da ita ne a ranar 21 ga watan Maris na shekarar da ta gabata a birnin Kigali, na kasar Rwanda, a ranar Lahadi ne yarjejeniyar ta fara aiki a hukumance.

Haka zalika a ranar Lahadin, Najeriya da jamhuriyar Benin suka rattaba hannu kan yarjejeniyar ta AfCFTA, kawo yanzu Eritrea ce kadai kasa daya tilo cikin mambobin kasashen Afrika 55 da bata sanya hannu kan yarjejeniyar ciniki maras shingen ta Afrika ba.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China