Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya bukaci Amurka ta sauya matsayarta game da batun nukiliyar Iran
2020-08-15 17:11:53        cri
Wakilin kasar Sin a MDD, Zhang Jun, a ranar Juma'a ya bukaci kasar Amurka da ta canza aniyarta game da batun dake shafar nukiliyar Iran kana ya nemi kasar ta gaggauta komawa kan tsarin gamayyar bangarori daban daban.

Da yake karin haske bayan da kwamitin sulhun MDD ya yi watsi da batun kudurin da Amurka ta gabatar na neman bukatar tsawaita wa'adin takunkumin da ta kakabawa Iran, Zhang ya ce, sakamakon kuri'ar kwamitin MDD ya nuna cewa, ra'ayin kashin kai ba shi da gindin zama, ba ya samun goyon baya, sannan cin zarafi ba zai yi tasiri ba. Duk wani yunkuri na neman fifita bukatar kashin kai sama da bukatun al'ummar kasa da kasa ba zai taba yin tasiri ba.

Zhang ya kara da cewa, a 'yan shekarun baya bayan nan, Amurka ta kara bayyana matsayinta na ra'ayin kashin kai da fifita kanta, Amurka ta yi watsi da nauyin dake bisa wuyanta na kasa da kasa, kuma ta janye daga yarjejeniyoyin kungiyoyin kasa da kasa, lamarin da ya kara zubar mata da kimarta a idanun kasa da kasa.

Sin ta bukaci Amurka da ta yi watsi da ra'ayin kashin kai kana da dena daukar matakan sanya takunkumi da kafa dokokin dake shafar mallakar makamai a bisa ra'ayin kashin kanta. Ya kamata Amurka ta mayar da hankali kan kyautata halayayyarta bisa hakikanin gaskiya, kuma ta gaggauta dawowa kan hanya mafi dacewa game da batun yarjejeniyar makaman nukiliyar kasar Iran bisa kudurin kwamitin sulhun MDD mai lamba 2231, wanda aka amince da shi a shekarar 2015 tsakanin kasar Iran da manyan kasashen duniya shida, da suka hada da Birtaniya, Sin, Faransa, Jamus, Rasha da Amurka. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China