Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres: Wajibi ne a sanya 'yan asalin wurare a yaki da COVID-19
2020-08-10 10:14:41        cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, wajibi ne a sanya 'yan asalin mazauna wurare da ma shiga a dama da su, a yaki da cutar COVID-19 gami da taswirar farfadowar da aka tsara.

Guterres wanda ya bayyana haka, yayin bikin ranar 'yan asalin mazauna wurare ta kasa da kasa, ya kuma ja hankalin duniya kan yadda annobar ta yi mumman taisiri kan irin wadannan rukunin jama'a dake zaune a sassa daban-daban na duniya.

Jami'in na MDD ya kara da cewa, a yayin da wadannan mutane ke fama da rashin daidaito, da nuna kyama da wariya gabanin wannan annoba, yanzu haka kuma suna fama da karancin kayayyakin kiwon lafiya, da ruwa mai tsabta da karuwar rauni a fannin rashin tsaftar muhalli.

A don haka, ya yi kira ga kasashen duniya, da su yi amfani da albarkatun da Allah ya hore musu wajen kula da bukatun su, su kuma martaba irin gudummawar da suke bayarwa, a kuma mutunta 'yancinsu na halal. Yana mai cewa, wajibi ne a rika tuntubarsu, a dukkan kokarin da ake na ginawa da yadda za a sake farfadowa yadda ya kamata. Ya ce, tun lokacin da cutar ta barke a duniya, hukumomin MDD ke kokari wajen kare 'yancin 'yan asalin mazauna wurare.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China