Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Biyu cikin biyar na makarantun duniya ba su da kayayyakin wanke hannu a shekarar 2019
2020-08-14 12:34:57        cri

Wani rahoton bincike na MDD ya gano cewa, biyu daga cikin biyar wato kashi 43 bisa 100 na makarantun dake fadin duniya suna da karancin muhimman kayayyakin wanke hannu wato sabulu da ruwa a shekarar 2019, wadanda su ne muhimman sharruda da suka kamata makarantun su cika kafin samun damar bude makarantun a lokacin da ake fama da annobar COVID-19.

Kimanin yara miliyan 818 ne suke da karancin muhimman kayayyakin wanke hannu a makarantunsu, wanda hakan ya jefa su cikin hadarin kamuwa da cutar COVID-19 da sauran cutuka masu yaduwa, kamar yadda rahoton da asusun kula da kananan yara na MDD wato UNICEF da hukumar lafiya ta duniya WHO suka fitar a ranar Alhamis.

Sama da kashi daya bisa uku na wadannan yara wato yara miliyan 295 sun fito ne daga yankin kudu da hamadar saharar Afrika.

A kasashen da suke da karancin ci gaba, bakwai daga cikin 10 na makarantun suna fuskantar karancin muhimman kayayyakin wanke hannu, kana rabin adadin makarantun suna da karancin muhimman kayayyakin tsaftar muhalli da rashin ruwa, a cewar rahoton mai taken, "Ci gaba game da samar da ruwan sha, tsaftar muhalli da tsaftar makarantu".

A jimlace, daya daga cikin makarantu uku a duk duniya suna da ko karancin kayayyakin samar da ruwan sha ko kuma sam ba su da kayayyakin samar da ruwan shan baki daya. Kusan yara miliyan 698 ne suke fama da karancin muhimman kayayyakin tsaftar muhalli a makarantunsu. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China