Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masani: WHO tana tattaunawa da Rasha kan batun rigakafi
2020-08-14 12:51:40        cri

Wani kwararren masanin hukumar lafiya ta duniya WHO ya bayyana a ranar Alhamis cewa, a halin yanzu ana ci gaba da tattaunawa da kasar Rasha domin samun karin bayanai game da alluran rigakafin cutar COVID-19 wanda Rashan za ta fara samarwa nan ba da jimawa ba.

Dakta Bruce Aylward, babban mashawarci ga darakta janar na hukumar WHO, ya fadawa taron manema labarai cewa, har yanzu hukumar WHO ba ta da isassun bayanan da za ta iya yanke hukunci kan batun rigakafin na Rasha.

Ya fadawa 'yan jaridu cewa, a karkashin kulawar hukumar WHO, akwai rigakafi guda tara da aka gabatarwa hukumar ya zuwa yanzu, domin neman shiga matakan gwaji na biyu da na uku, amma rigakafin na Rasha ba ya daya daga cikin guda taran da aka gabatar.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar a ranar Talata cewa, kasarsa ta samar da rigakafin cutar COVID-19 dake sahun farko a duniya.

Daga bisani a ranar Laraba, ministan kiwon lafiya na kasar Rasha Mikhail Murashko ya ce, kasar za ta fara samar da rigakafin cutar cikin makonni biyu. Murashko ya kara da cewa, babu wani shakku game da sahihancin rigakafin. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China