Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Sin da Rasha sun tattauna ta wayar tarho yayin da ake cika shekaru 75 da samun nasarar kawo karshen yakin duniya na 2
2020-05-09 17:09:19        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a jiya Juma'a, dangane da cika shekaru 75 da samun nasarar kawo karshen yakin duniya na 2.

A cewar shugaba Xi, kasar Sin ta shiryawa hada hannu da Rasha domin tsare nasarorin da aka cimma a yakin, da kuma tabbatar da adalci da daidaito da goyon baya, kana da gudanar da hulda tsakanin kasa da kasa da kuma ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da bada gudunmuwa wajen samar da ci gaba a duniya.

Da ya yi tsokaci kan yadda al'ummomin duniya ke yaki da annobar COVID-19 a yanzu, shugaba Xi ya ce karkashin jagorancin Shugaba Putin, matakan Rasha na dakile cutar da kandagarkinta, sun fara tasiri sannu a hankali.

A nasa banagren, Shugaba Putin ya ce, al'ummomin Rasha da Sin sun yi gagarumar sadaukarwa wajen cimma nasarar kawo karshen yakin duniya na biyu. Ya ce bisa la'akari da murnar cika shekaru 75 da nasarar kawo karshen yakin a shirye Rasha take ta karfafa hadin gwiwa da Sin da kuma aiwatar da matsayarsu ta tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Da yake godewa kasar Sin bisa samarwa Rasha agajin jin kai da kayayyakin kariya, shugaba Putin ya ce a shirye Rasha take, ta dauki darasi daga matakan kasar Sin na dakilewa da kandagarkin annoba, da kuma hada kai da ita wajen gudanar da bincike da samar da alluran rigakafi.

Ya kara da cewa, Rasha na adawa da yunkurin wasu na amfani da annobar wajen dorawa Sin laifi, yana mai cewa, kasarsa na tare da Sin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China