Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rasha: Tilastawa kasar Sin rufe karamin ofishin jakadancinta da Amurka ta yi, ya sabawa ka'idar gudanar da aiki bisa doka da shari'a
2020-07-24 13:21:03        cri

Jiya Alhamis, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha, Maria Zakharova ta shedawa manema labarai cewa, gwamnatin Amurka ta nemi kasar Sin da ta rufe karamin ofishin jakadancinta dake birnin Houston, matakin da ya sabawa ka'idar gudanar da aiki bisa doka da shari'a da Amurka ke ikirarin aiki da shi a yau da kullum.

A cewarta, idan wata kasa ta kiyaye muradunta bisa hanyar da ta dace da raya tattalin arzikinta yadda ya kamata ba tare da sabawa tsarin dokar kasar Amurka ba, to, Amurka za ta rika yi mata katsalandan, kamar yin barazana da yanke hukunci har ma da cin zali da kuma cafke mutane da kwashe dukiyoyi da dai sauransu. Amurka ta sha neman wasu kasashe su rufe ofishi ko karamin ofishin jakadancinsu a kasar, kuma ba gwamnatin Donald Trump ce kadai ta yi amfani da wannan mataki ba a shekarun baya-baya nan, matakin da ya sabawa akidun da Amurka ke ikirarin tana dauke da su a duniya yau da kullum. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China