Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Putin: An yi rajistar allurar rigakafin cutar COVID-19 ta farko a Rasha
2020-08-12 13:58:30        cri

Ranar 11 ga wata, shugaba Vlładimir Putin na kasar Rasha ya ce, ma'aikatar lafiyar kasar ta yi rajistar allurar rigakafin cutar COVID-19 ta farko, wanda Rasha ta kirkiro. An kuma yi wa diyyarsa allurar, kuma tana cikin koshin lafiya a halin yanzu. Putin ya yi fatan cewa, nan ba da dadewa ba, za a samar da allurar masu yawa.

Wani rahoton da shugaban Rasha ya wallafa ranar 11 ga wata a shafinsa na Intanet, ya bayyana cewa, yayin wata ganawa da ya yi da wasu jami'an gwamnatin kasar ta kafar bidiyo a fadar shugaban kasar a jihar Moskovskaya, Putin ya nuna cewa, an riga an yi bincike kan wannan allurar da cibiyar nazarin cututtuka masu yaduwa da kananan halittu ta Gamaleya ta Rasha ta yi nazari a kai. Allurar tana samar da garkuwa ga jikin dan Adam yadda ya kamata.

Kafofin yada labaru na Rasha sun ruwaito cewa, yanzu hukumomin nazarin kimiyya guda 17 ne suke nazari kan allurar iri iri a kalla 26 a Rasha. Cibiyar Gamaleya ita ce take gaban wajen samar da allurar. Kamar yadda aka tsara, a wannan watan, cibiyar za ta fara gwajin alluran kan bil-Adama a mataki na uku na tsawon watanni 5 a kan baligai dubu 2. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China