Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rasha: Ra'ayin "raya kyakkyawar makomar Bil Adama bai daya" da Sin ta gabatar na da mana'a sosai ga hadin kan kasa da kasa
2020-04-15 11:10:52        cri

Jiya Talata agogon Rasha, ministan harkokin wajen kasar Sergey Lavrov, ya zanta da kafofin yada labarai na Rasha da na ketare a kan Intanet, kan wasu batutuwa mafiya jawo hankalin kasa da kasa. Inda Lavrov ya nuna cewa, tallafin da kasarsa ta baiwa sauran kasashe, ya sa ana nuna mata kiyayya. Lallai wannan batu ne mai matukar bacin rai, kuma tunanin zai tsananta kalubaloli daban-daban da ake fuskantar, to sai dai kuma a cewar sa, ra'ayin raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya da Sin ta gabatar, na da babbar ma'ana wajen hadin kan kasa da kasa.

Lavrov ya kuma kara da cewa, zancen da ake yi wai ya kamata a hana bunkasuwar Rasha da Sin, da ma wasu sauran kasashe ba shi da kyau ko kadan, zai kuma iya yin illa ga dangantakar bangarorin daban-daba. Irin wannan tunani da ake yi duk karairayi ne, kuma babu shakka zai tsananta kalubaloli dake dabaibaye duniya.

Ban da wannan kuma, Lavrov ya ce bayan an samu nasara kan cutar COVID-19 gaba daya, ya kamata a sake kimanta kwarewar kasa da kasa, da kuma kungiyoyin bangarori daban-daban, na daidaita barazana dake illata dukkanin duniya da gudunmawar da suka bayar. Ya ce, wannan tunanin da Sin ta gabatar na raya kyakkyawar makomar Bil Adama bai daya, zai kara samar da ma'ana a nan gaba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China