Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Darektan Africa CDC ya yi kira da a karfafa hadin gwiwa don yakar COVID-19 a Afirka
2020-08-13 10:14:31        cri

Darektan cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC) John Nkengasong, ya yi kira ga kasashen nahiyar da ma duniya baki daya, da su karfafa hadin gwiwa, wajen ganin hana yaduwar cutar COVID-19 a nahiyar Afirka.

Nkengasong wanda ya jaddada bukatar yin aiki tare da kulla alaka bisa manufa a Afirka da ma duniya baki daya, ya kuma yabawa gwamnati da kamfanonin kasar Sin, kamar gidauniyar Jack Ma da Alibaba, bisa ga taimakon da suke bayarwa a yaki da annobar COVID-19 a Afirka.

Ya ce, kimanin kaso 63 cikin 100 na kasashen Afirka, sun ba da rahoton kasa da mutane 5,000 da suka kamu da cutar, sai dai ya jaddada cewa, har yanzu Afirka na da kyakkyawar dama na kara karfin yaki da wannan annoba.

Jami'in ya ce, adadin wadanda aka yiwa gwajin cutar a Afirka, abin karfafa gwiwa ne, inda ya zuwa yanzu aka yiwa sama da mutane miliyan 9 gwajin cutar. Sai dai kuma, darektan cibiyar ya jaddada cewa, akwai bukatar kasashen Afirka su kara karfin yin gwajin cutar. Yana cewa, akwai bukatar nahiyar, ta yiwa kimanin mutane miliyan 15 gwajin cutar a ko wane wata, kafin ta ga bayan annobar.

Africa CDC ta bayyana cewa, ya zuwa jiya Laraba, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a Afirka ya kai 1,064,546, akwai kuma mutane 23,839 da cutar ta halaka. Kana yawan mutanen da suka warke daga cutar a nahiyar ya kai 758,292. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China