Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC tana shirin yiwa mutane miliyan 10 gwajin COVID-19 cikin watanni masu zuwa
2020-06-05 10:12:19        cri

Babban darektan cibiyar kandagarkin da hana yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC) John Nkengasong, ya bayyana shirin cibiyar na yiwa mutane miliyan 10 gwajin cutar COVID-19 a nahiyar nan da watanni masu zuwa.

Darektan wanda ya bayyana haka Jiya Alhamis, yayin wani taro da aka kira ta kafar bidiyo, ya ce, shirin gwajin mai suna PACT, ya kunshi muhimman sassa guda uku, da suka hada da yiwa mutane gwajin cutar, gano wadanda suka kamu da cutar da ma wadanda suka yi mu'amula da su, da samar musu da magani gami da tallafawa marasa lafiya.

Manufofin shirin gwajin cutar ta COVID-19 da cibiyar ke fatan gudanarwa a nahiyar, sun hada da yiwa mutane miliyan 10 gwajin COVID-19 cikin 'yan watanni masu zuwa, da tura ma'aikatan lafiya miliyan 1 don tafiyar da shirin, da horas da ma'aikatan lafiya dubu 100 don ganin shirin ya samu nasara.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China