Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Afrika sun yabawa taimakon gidauniyar Jack Ma don yaki da COVID-19
2020-04-05 16:57:58        cri

Shugabannin kasashe da hukumomin gwamnatocin Afrika sun yabawa taimakon kayayyakin kiwon lafiya wanda gidauniyar Jack Ma da ta Alibaba suka baiwa nahiyar domin yaki da annobar COVID-19.

Sanarwar da hukumar gudanarwar AU ta fitar a wani taron da aka gudanar ta wayar tarho, shugabannin kasashen Afrika da hukumomin gwamnatocin kasashen sun yabawa tallafin da aka raba karkashin jagorancin firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed da kwamitin rabon kayayyakin tallafin na gidauniyar Jack Ma, tare da taimakon hukumar samar da abinci ta MDD (WFP) gami da cibiyar dakile yaduwar cutar ta Afrika CDC, kayayyakin sun hada da na'uorin gwaje-gwaje miliyan 1, da takunkumin rufe fuska miliyan 6, da rigunan kariya dubu 600, wanda aka rabawa dukkan kasashen Afrika a cikin kasa da mako guda.

Taron shugabannin kasashen na Afrika ta wayar tarho, wanda shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, ya jagoranta wanda kuma shi ne shugaban kwamitin taron AU a halin yanzu, ya samu halartar shugaban kasar Masar Abdel Fattah al Sisi, da na Mali Ibrahim Boubacar Keita, da na Kenya Uhuru Kenyatta, Felix Tshisekedi na DRC, da na Rwanda Paul Kagame, da firaministan Habasha Abiy Ahmed, da shugaban kasar Senegal Macky Sall, sai kuma na kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China