Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta yi yi hasashen samun raguwar yaduwar COVID-19 a Afrika
2020-05-15 10:34:50        cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi hasashen raguwar adadin masu kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 a Afrika, sannan yanayin kai wa kololuwar cutar zai zo sannu a hankali a galibin kasashen nahiyar, biyo bayan karuwar nasarar matakan yaki da ita.

Daraktar WHO a nahiyar Afrika, Matshidiso Moeti, ta ce an sake nazarin ne bisa nasarar da aka samu daga wasu matakai da gwamnatoci ke aiwatarwa, kamar wani bangare na matakin kulle da nisantar taron jama'a da wanke hannu.

Ta ce wani nazarin da hukumar ta yi, ya nuna cewa adadin masu kamuwa da COVID-19 a Afrika zai kai matsayin koli cikin makonni 5 da samun bullar cutar na farko a wata kasa, kuma a matsakaicin mataki, kimanin kaso 26 na al'ummar nahiyar, za su kamu da cutar.

Jami'ar ta bayyana cewa, an yi wannan nazari ne bisa la'akari da yanayin yaduwar cuta a cikin al'umma, musammam a yankunan karkara. Amma kuma sun ga yadda gwamnatocin nahiyar suka dauki matakai da suka rage yaduwar cutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China