Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Ana samun karuwar yaduwar cutar a nahiyar Afrika, musamman a yankunan karkara
2020-04-11 16:08:54        cri

Darakta Janar na hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce hukumar ta lura ana samun karuwar yaduwar cutar a wasu kasashe, musamman a nahiyar Afrika, inda kwayar cutar ke bazuwa a yankunan karkara.

Ya ce yanzu ana samun karuwar masu kamuwa da cutar a kasashe fiye da 16. Yana mai cewa za a kara samun matsi kan tsarukan kiwon lafiya da suka tabarbare, musammam na yankunan karkara.

Tedros Ghebreyesus, ya kuma yi kira ga kasashen G20 su gaggauta taimakawa nahiyar Afrika, inda a yanzu adadin wadanda suka kamu ba shi da yawa, amma cutar na yaduwa cikin sauri.

Sai dai, Darakta Janar din ya ce hukumarsa ta lura ana samun raguwar masu kamuwa da cutar COVID-19 a kasashen da cutar tafi kamari a nahiyar Turai.

Kawo yanzu, WHO ta bada rahoton mutane miliyan 1.5 ne aka tabbatar sun harbu da cutar a duniya, inda ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 92,000. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China