Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Rasha ya amince da kiran taron kolin kasashen Rasha, Turkiyya, Faransa da Jamus kan batun Syria
2020-02-24 11:22:34        cri
Sakataren watsa labarai na shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov ya bayyana a jiya Lahadi cewa, shugaban kasar Vladimir Putin ya nuna goyon bayansa kan gudanar da taron koli tsakanin bangarori hudu da suka hada da Rasha, Turkiyya, Faransa da Jamus kan batun Syria.

Ya kuma kara da cewa, a halin a yanzu, bangarorin hudu suna tattaunawa game da lokacin da zasu kira taron. Ya ce, ya zuwa yanzu, kasar Turkiyya bata aiwatar da yarjejeniyar da shugabannin kasashen Rasha da Turkiyya suka kulla a birnin Sochi na kasar Rasha a shekarar 2018 ba.

Bisa labarin da aka samu, an ce, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana a ranar 21 ga wata cewa, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Dorothea Merkel sun bada shawarar kiran taron kolin kasashen Rasha, Turkiyya, Faransa da Jamus kan batun Syria a ranar 5 ga watan Maris mai zuwa a birnin Istanbul na kasarTurkiyya.

Lardin Idleb na kasar Syria yana iyaka da kasar Turkiyya, wanda ya kasance yanki na karshe da dakaru masu adawa da gwamnatin kasar Syria da kungiyar masu tsatsauran ra'ayi suka mamaye cikin kasar Syria. Sojojin gwamnatin kasar Syria suna fatan dawo da wannan yanki karkashin ikonsu. A watan Satumban shekarar 2018, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan sun yi ganawa a birnin Sochi, inda suka yanke shawarar kafa wani yanki wanda ba na harkar soji ba a tsakanin sojojin gwamnatin kasar Syria da dakaru masu adawa da gwamnati a lardin Idleb. Kuma bisa yarjejeniyar kasashen, Turkiyya zata kafa tashoshin sa ido guda 12 domin sa kaimi da a tsagaita bude wuta.

Kwanan baya, sojojin gwamnatin kasar Syria da sojojin kasar Turkiyya sun yi musayar wuta kai tsaye a wannan lardin, wanda ya halaka tare da jikkata mutanen bangarorin biyu.(Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China