Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Buhari: Mayakan Boko Haram ba su fi sojojin Najeriya makamai ba
2020-08-12 10:52:42        cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya karyata ikirarin da wasu ke yi cewa, mayakan Boko Haram sun fi gwamnati da ma sojojin kasar kudi da makamai.

Shugaban wanda ya bayyana haka yayin taron tsaro da ya gudanar da gwamnonin jihohi da manyan hafsoshin tsaron kasar, ya bayyana cewa, an ci lagun 'yan ta'addan a halin yanzu, inda ya bayyana su a matsayin mayunwata, dake neman abinci ido rufe, inda suke wawushe shaguna da kasuwanni da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Sai dai kuma, ya bayyana damuwa kan yadda kananan makamai ke shiga hannun kungiyoyin bata gari da 'yan ta'adda. Haka kuma, shugaba Buhari, ya bayyana gamsuwa kan yadda kasashe makwabta ke ba da hadin kai a yakin da ake yi da 'yan ta'addan.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China