Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Nijeriya sun kashe mayakan BH 16 a yankin arewa maso gabashin kasar
2019-11-16 15:35:32        cri
Mayakan Kungiyar BH akalla 16 aka kashe, yayin da suke kokarin shiga sansanonin 2 na sojojin Nijeriya a yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da rikici.

Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin Aminu Iliyasu, ya ce mayakan sun yi yunkurin kai hari ne sansanonin soji a wasu wurare biyu dake yankin Abadam na Jihar Borno.

Aminu Iliyasu, ya ce 'yan ta'addan na dauke ne da ababen fashewa, da motocin yaki masu sulke da makaman roka da sauran wasu kananan makamai.

Ya ce nan da nan zaratan sojojin suka mayar da martini, inda suka ci karfinsu tare da kashe wasu, lamarin da ya tilastawa 'yan ta'addan janyewa.

Ya ce duk da haka, galibin 'yan ta'addan sun tsere da raunikan harbi masu tsanani domin an ga alamun jini a hanyar da suka bi wajen tserewa.

Kakakin ya ce yayin arangamar, an kashe soja guda yayin da wasu 4 kuma suka raunana. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China