Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakarun sojin Najeriya sun hallaka 'yan Boko Haram 3 yayin wani dauki ba dadi
2019-11-28 09:59:42        cri

A jiya Laraba ne rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa, dakarun ta sun hallaka mayakan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram, yayin wani dauki ba dadi da sassan biyu suka yi, a yankin Sabon Gari, a kan hanyar mayakan ta ratsa dajin Sambisa dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojojin dake yankin Aminu Iliyasu, ya ce yayin bata kashin na ranar Talata, da dama daga mayakan sun tsere cikin dajin dauke da raunukan harbin bindiga.

Jami'in ya kara da cewa, yayin arangamar sojojin sun gano cewa, mayakan na tare da wasu mutane da ke taimaka musu, wajen jigilar abinci da sauran kayayyakin bukata na yau da kullum zuwa dajin na Sambisa.

Bayan fatattakar mayakan, sojojin sun kuma kwashe kayayyakin abinci, da babura, da albarusai, wadanda mayakan na Boko Haram suka gudu suka bari. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China