Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram da dama a yankin arewa maso gabashin kasar
2020-06-30 13:14:48        cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram da dama, yayin wasu jerin hare-hare ta sama da suka kaddamar a jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun rundunar sojojin kasar John Eneche, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, harin na ranar Asabar da dakarun suka kaddamar, ya biyo bayan wani shawagin sanya-ido ta sama da sojojin suka gudanar a wani maboyar 'yan ta'addan da a baya suke amfani da shi wajen kai hare-hare kan fararen hula.

Enenche, ya ce, an yi amfani da jiragen yaki guda biyu ne wajen kai wadannan hare-hare, inda suka yi nasarar lalata sansanoni da dama na 'yan ta'addan, baya ga karya lagon wasu daga cikinsu.

Tun a shekarar 2009 ne, kungiyar Boko Haram ke kokarin kafa daular Islamaya a yankin arewa maso gabashin kasar, inda ta fadada hare-haren da take kaiwa zuwa kasashen dake yankin Tafkin Chadi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China