Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojin Nijeriya ta lalata cibiyar sarrafa dabarun yaki ta BH tare da kisan wasu mayakan kungiyar
2020-06-20 16:16:27        cri
Rundunar sojin Nijeriya ta sanar a jiya cewa, jerin luguden wuta ta sama da ta yi, sun yi sanadin lalata cibiyar sarrafa dabaru ta BH tare da kisan wasu mayakan kungiyar.

Kakakin rundunar John Enenche, wanda ya tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwar da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce an yi luguden wutan ne a ranar Laraba a yankin Yuwe, wani bangare na dajin Sambisa dake jihar Borno na arewacin kasar.

John Enenche, ya ce aikin na ranar Laraba, wani bangare ne na ayyukan soji ta sama da ake ci gaba da yi da nufin karya lagon kungiyar.

Ya ce matakin ya kai ga lalata cibiyar gudanar da ayyukan kungiyar da kewayenta, tare kuma da kisan mayaka da dama. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China