Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya: tsoffin 'yan Boko Haram sun koma cikin al'umma bayan samun horon gyara halayya
2019-11-28 09:28:24        cri
Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta shigar da a kalla tsofaffin mambobin kungiyar Boko Haram 983 cikin al'umma, bayan da suka samu cikakken horon gyara halayya, karkashin shirin da rundunar ta yiwa lakabi da "Operation Safe Corridor", wanda ya gudana a jihar Gombe dake arewa maso gabashin kasar.

Da yake tabbatar da hakan, kwamandan rundunar sojojin yankin Olusegun Adeniyi, ya ce mambobin kungiyar da aka sallama sun hada da wadanda suka mika kansu ga dakarun sojin kasar a sassa daban daban, tare da nuna nadamar kasancewa 'yan kungiyar ta Boko Haram.

Olusegun Adeniyi, wanda ya bayyana hakan yayin bikin mika mutanen ga gwamnatin jihar Borno wadda za ta shirya sada su da iyalan su, ya ce tsoffin 'yan Boko Haram din sun hada da mata 5, kuma sai da rundunar sojojin ta tabbatar sun rabu da akidar ta'addanci a tsawon watanni 12 da suka yi suna samun kulawa, kafin a kai ga yanke kudurin sakin su.

Ya ce rundunar sojojin ta amince da sauyin halayyar mutanen, kuma an tabbatar da cewa, ba su da wata sauran alaka da mayakan Boko Haram, za kuma su kasance masu bin doka da oda yayin da suke fara sabuwar rayuwa. Kaza lika yayin da suke tsare, an koyar da su sana'o'in dogaro da kai, wadanda za su ba su dama tsayawa da kafafun su bayan komawa cikin al'umma. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China