Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya taya Lukeshenko murnar lashe zaben shugabancin kasar Belarus
2020-08-10 16:25:30        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kira Alexander Grigorievich Lukashenko ta wayar tarho Litinin din nan, domin taya shi murnar sake zabensa a matsayin shugaban kasar Belarus.

A cikin sakon nasa na taya murna, Xi Jinping ya ce a shirye yake ya yi aiki kafada da kafada da shugaba Lukashenko, domin ciyar da alakar Sin da Belarus bisa manyan tsare-tsare gaba, da bude wasu sabbin makoma na alakar cin moriyar juna tsakanin kasashen biyu a fannoni daban-daban da samar da sabbin damammaki ga kasashen biyu da kuma al'ummominsu. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China