![]() |
|
2020-08-05 19:37:08 cri |
Shugaban kasar Sin Xi jinping, ya aikawa takwaransa na kasar Lebanon Michel Aoun sakon ta'aziya Larabar nan, dangane da mummunar fashewar da ta auku a Beirut, fadar mulkin kasar Lebanon.
A cikin sakon, shugaba Xi ya ce ya kadu da samun labarin fashewar da ta auku a Beirut, wadda ta yi sanadiyar rayuka da dama.
A madadin gwamnatin kasar Sin da al'ummar Sinawa, da shi kansa, Xi ya mika sakon ta'aziya ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, tare da jajantawa iyalan wadanda suka jikkata da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.(Ibrahim)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China