Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin zamanantar da tsaron kasa da rundunonin tsaro
2020-08-01 16:30:48        cri

Xi Jinping, sakatare Janar na kwamitin tsakiya na JKS kuma shugaban kasar Sin, ya nanata muhimmancin kara zamanantar da tsarin tsaron kasa da rundunonin tsaro.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne lokacin da yake jagorantar wani zaman nazari na ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, kan karfafa zamanantar da tsaron kasa da rundunonin tsaro, wanda ya gudana a ranar Alhamis.

Ya ce ya kamata zamanantar da harkar tsaro ya tafi tare da aikin zamanantar da kasa, sannan dole ne karfin rundunar soji ya dace da muhimman muradun kasa.

Shugaban na Sin ya kara da cewa, a bana, kasar Sin za ta cimma burika da manufofin karfafa tsaron kasa da rundunonin tsaro na 2020, da shiga sabon babi domin kammala wannan aikin da kuma sauya rundunar sojin kasar ta yadda za ta yi gogayya da na kasa da kasa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China